Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Zika Na Ci Gaba Da Karuwa Kamar Wutar Daji


Severina Raimunda holds her granddaughter Melisa Vitoria, left, who was born with microcephaly and her twin brother, Edison Junior, at the IMIP hospital in Recife, Pernambuco state, Brazil, Feb. 3, 2016.
Severina Raimunda holds her granddaughter Melisa Vitoria, left, who was born with microcephaly and her twin brother, Edison Junior, at the IMIP hospital in Recife, Pernambuco state, Brazil, Feb. 3, 2016.

Cutar nan da ake kira Zika yanzu sai bazuwa takeyi kamar wutar daji a kudanci da tsakiyar kasashen latin Amurka dama yankin karebiya.

A cewar masana, lamarin da ban tsoro domin ko tana da nasaba da tauyewar kwakwalwan jarirai.

Ana haihuwar jarirai a inda cutar take da kananan kawuna domin kwakwalwar su ta bar aiki.

Ba wanda yasan irin halin da wadannan jarirai da aka Haifa cikin wannan yanayi suke shiga.

Kwararru suka ce idan baya ga cewa cutar tana da nasaba da haihuwar jariran da kananan kai da ba a saba gani wanda yake hana kwakwalwar su aiki yadda ya kamata ba to da cutar ta zika ba wata barazana bace.

An baiwa cutar suna zika ne domin a dajin zika dake kasar Uganda ne aka fara gano ta shekaru da yawa da suka gabata, inda daga nan cutar ta yadu zuwa kudu maso gabashin Asiya, kafin ta tsallaka zuwa yankin Fasific har takai ga kasar Brazil.

Cutar Zika dai sabuwa ce fil ga Amurkawa, domin basu santa ba kuma basu da kariya game da ita.

Sai dai irin Sauron da ke yada wannan cutar ta zika yana bazuwa sosai a kasar Brazil inda ake da cicirindon mutane.Shi wannan Sauron yana rayuwa ne cikin ruwan datti, kuma bai taran karancin ruwa da zai yi kwai a ciki kana yana cizo ba dare ba rana.

Dr.Anthony Fauci wanda masani ne cibiyar nazarin cututtuka da yaduwar su yace ba don haihuwar yaran da akeyi da kananan kai ba kuma kwakwalwar su tana samun matsala ba da kila ma ba za a lura da cutar ba har taci ta kare.

XS
SM
MD
LG