Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cututtukan Da Suka Fi Yawan Kashe Mutane a Fadin Duniya


A fadin duniya mutane bakwai cikin goma na mutuwa ne sanadiyar cututtukan da suka hada da hawan jini da ciwon daji da ciwon siga da mummunan ciwon huhu, a cewar wani bincike da aka kafe a fitatciyar mujallar The Lancet cikin wannan watan.

Wadannan cututtuka ba wai kawai suna saurin kashe mutane bane, jinyarsu na da tsadar gaske. Binciken da aka kafe a mujallar The Lancet, ya kimanta cewa cikin shekaru 15 masu zuwa, kasashe masu tasowa zasu kashe sama da dalar Amurka Triliyan bakwai kan wadannan cututtuka.

Shekaru uku da suka gabata, shugabannin duniya sunyi alkawari rage samun mace-mace daga ire-iren wannan cututtuka da ake samu da kashi daya cikin uku zuwa shekarar 2030.

A taron babban zauren MDD na ranar Alhamis, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya, Dakta Tedros Adhanom, ya ce kasasehn duniya ‘kasa da rabi zasu samu iya cimma wannan manufa, yana mai kiran shugabannin duniya da su bayar da himma kan wannnan batu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG