Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Kasar Yigoslabiya Zasu Kada Kuri'ar Raba Gardama


Tsohuwar kasar Yugoslabiya, na wani sabon yunkurin sauya sunan kasar, don warware matsalar da taki ci taki cinnyewa har tsawon shekaru 27.

Ranar Lahadi 30 ga watan Satunba, al’ummar tsohuwar kasar Yugoslav, Jamhuriyar Macedonia, zasu jefa kuri’ar raba gaddama ta Eh ko A’a, don sauya sunan kasar zuwa Jamhuriyar Arewacin Macedonia, daya daga cikin manyan matakai don warware tsohon rikici na shekaru 27 tsakanin su da kasar Greece, wanda ke da wani yanki dake da irin wannan sunan.

Yin hakan al’ummar Macedonia zasu bude wani sabon babi wanda zai basu damar shiga kungiyar NATO da ta kasashen Turai. Jiya Laraba a wajen wani gangami kafen kawo karshen yakin neman zabe, Firaministan Macedonia Zoran Zaev, ya bayyana cewar al’ummar kasar kansu a hade yake, kuma yana da yakinin cewar, yawancin su zasu amsa cewa sun yadda su shiga cikin yankin Turai.

Kasar na yunkurin farfadowa daga rikicin tattalin arziki na shekaru 2, da matsalolin rashin aikin yi da ya dara kashi 20% cikin 100%, kana da matsalar karancin albashi a yankin.

Yayin da kuri’u ke nuna gaggarumin goyon baya neman sauyi, akwai damuwa akan rashin fitowar jama’a, daga bangaren masu ra’ayin rikau na kasar, wanda basu yadda da sauyin sunan na kasar ba, sun bukaci a kauracewa kuri’ar raba gaddamar.

Adadin da kawai ake bukatar su fito, akalla kashi 50% na masu jefa kuri’ar don amincewa da sauyin sunan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG