Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama Direban Da 'Yan Sandan Spain Ke Nema An Kashe Shi


'Yan Sanda a Spain
'Yan Sanda a Spain

Mai yiwa ne an kashe direban da motar da ya kai hari ya kashe mutane a birnin Barcelona ranar Alhamis.

‘Yan sanda a Spain sunce mai yiwuwa direban da ya rafkawa mutane mota suna tafiya da kafa a kan titin Barcelona ranar alhamis ya arce, sabanin rahotannin da aka bayar tun farko cewa direban na daga cikin wadanda aka kashe a irin wannan harin bayan ‘yan sa’oi a wani gari dake kusa.

Ana kyautata zaton Younes Abouyaaqoub mai shekaru 22 dan asalin kasar Morocco da ‘yan sanda k enema ruwa a jallo, shine shugaban kungiyar da ta kai hari a Barcelona da kuma wani birni a Cambrils.

A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin kasashen ketare na kasar Jamus Sigmar Gabriel ya ziyarci Las Ramblas Boulevard yau asabar domin ajiye furanni a inda ake tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a Barcelona.

Gabriel yayi kira da a kara hada kai a kasashen turai da kuma sauran kasashen duniya a yaki da ta’addanci.

Mun sani ‘yan ta’adda na kokarin cusa tsoro da yayata tashin hankali. Mun fuskanci haka bara a kasuwar Kirsimeti dake birnin Berlin. Muna bukatar taimakon wadanda harin ya shafa da danginsu yanzu. Banda haka kuma, muna bukatar kara hada kai a kasashen turai, kamar yadda muka yi a lokutan baya. Sai dai abin takaici shine, babu yadda za a iya tabbatar da kariya daga wadannan matsoratan ‘yan kisan. Abinda ya kamata mu fahimta ke nan.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG