Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Amurka da Rasha Zasu Cimma Yarjejeniya kan Syria


Hayaki da ya tashi bayan jiragen sama sun kai hari a Syria

Akwai yiwuwar Amurka da Rasha zasu sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin tabbatar da kare jiragen sama a sararin samaniyar Syria. Yau talata ake sa ran zasu sanya hannu, kamar yadda bayanai da ma'aikatar tsaron Amurka ta bayar suka yi nuni.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Keftin na mayakan ruwan Amurka Jeff Davis, ya jaddada cewa wadan nan sharudda ne ba wani bangare na yarjejeniya ba ne kan yadda kasashen biyu zasu yi aiki a Syria ba. An tsara sharuddan ne da zummar hana jiragen yakin Amurka dana Rasha yin karo a sararin samaniyar Syria inda kasashen biyu suke kai hare hare da jiragen saman yaki.

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya gayawa Muryar Amirka cewa, takardun sharuddan zasu kunshi bayanai kan tashoshin da matukan jiragen zasu rika magana da juna, da kuma wasu matakai na kiyaye lafiya yayinda kasashen biyu suke shawagi a sararin samaniyar Syria.

Rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagora tana auna hare harenta ne fiye da shekara daya yanzu kan muradun kungiyar mayakan sa kai na ISIS.

Ita ma Rasha ta fada cewa kungiyar ISIS take aunawa da wasu kungiyoyin yan ta'adda, amma ma'aikatar tsaron Amurka da kungiyoyin kare hakkin bil' Adama a Syria din suka ce hare-haren da Rasha take kaiwa basu kai wa wuraren da ISIS take iko dasu ba.

XS
SM
MD
LG