Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Jam'iyyar ANC Ta Afrika Ta Kudu Ita Zata Lashe Zabe


A kasar Afrika Ta Kudu, Dukkan alamu na cewa Jam’iyyar ANC wato (African National Congress) na dab da sake lashe zabe don ci gaba da rike kujerar shugabancin kasar a karo na shidda a jere, bayan zaben ‘yan majalisar dokoki da aka yi a ranar Larabar da ta gabata.

Zaben na wannna bana ai shine na shidda da aka taba yi a kasar tun daga lokacin da aka zo karshen akidar wariyar launin fata a shekarar aluf dari tara da cisa’in da hudu.

Bayan samun sakamakon kashi 76 cikin 100 na kuri'un da aka kada a ranar Jumma'ar data gabata, jam’iyyar ANC, wadda ita ce jam’iyyar shugaban kasar Cyril Ramaphosa, ta sami kashi 57 cikin 100 na kuri'un da aka jefa. A shekarar 2014, jam’iyyar ANC ta samu kashi 62 cikin 100 na kuri'un.

Amma tabarbarewar tattalin arziki da kuma karuwar cin hanci da rashawa, ya batawa jam’iyyar suna, wanda ita ce jam’iyyar Nelson Mandela, shugaban kasar Afrika Ta Kudu bakin fata na farko. Wadannan Matsalolin suka sa wasu masu jefa kuri'a komawa zuwa jam'iyyun adawa.

Jam’iyyar DA wato (Democratic Alliance) ta samu kashi 22 cikin 100 na kuri'un, kamar yadda ta samu a shekarar 2014.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG