Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Za'a Kai Ruwa Rana Tsakanin Kusoshin APC a Jihohin Adamawa da Taraba


APC
APC

Akwai alamaun rikici zai barke tsakanin wasu kusoshin APC a jihohin Adamawa da Taraba

Batun ko su wanene yakamata a zaba wakilan jam'iyyar a zaben fitar da 'yan takara yana son ya zama wa jam'iyyar kadangaren bakin tulu.

Masu tallata Janaral Buhari a Adamawa da masu tallata Atiku Abubakar wanda dan asalin jihar ne suna karawa da juna. Alhaji Adamu Garbajo jami'in dake kula da kemfen na Buhari a jihohin Adamawa da Taraba ya bayyana dalilansu na tallatar da Bihari maimakon dansu Atiku Abubakar.

Yace a tarukan da suka yi a Yola da Jalingo jama'a sun nuna cewa a maganar tsaro babu wanda zai iya kubutar dasu sai Janaral Buhari. Akan maganar cin hanci kuma sai Janaral Buhari. Sun ce duk 'yan takaran dake neman shugaban kasa a karkashin APC mutanen kirki ne amma babu kaman Buhari. Idan har suna son su yiwa kasar adalci dole ne su hada hannu su roki sauran 'yan takarar su bar ma Buhari domin gaskiyarshi da rikon amana.

Amma magoya bayan Atiku sun ce su ne da nasara yayin da suka kuma musanta maganar cewa Atikun da magoya bayansa na shirin barin jam'iyyra APC. Sanata Aisha Jummai Alhasan dake neman tsayawa takarar gwamna a jihar Taraba tace ba haka zancen yake ba.

Sanata din ta zargi PDP da yin farfaganda cewa zata koma PDM. Tace idan da taso da tuni ta shiga PDM din domin an yi mata rajista kafin APC.

Amma kuma a jihar Adamawan akwai wadanda suka saba laya akan zargin wai rawar da Atiku ya taka wajen tsige gwamna Murtala Nyako.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG