Accessibility links

Da ba'Amurkiya da dan kasar Denmark na cikin koshin lafiya bayan an ceto su a kasar Somaliya

  • Ibrahim Garba

'Yan yammacin duniya- Jessica Buchanan da Poul Thisted da aka ceto

Hukumomin sojin Amurka sun ce wasu ‘yan yammacin duniya su biyu

Hukumomin sojin Amurka sun ce wasu ‘yan yammacin duniya su biyu – daya ‘yar Amurkiya daya kuma dan kasar Denmark – na cikin koshin lifiya bayan wasu dakarun musamman na Amurka sun kubutar da su daga hannun ‘yan bindiga a kasar Somaliya.

Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta fadi jiya Laraba cewa ana kula da lafiyar ba-Amurkiyar mai suna Jessica Buchanan a wani asibitin soji da ke Djibouti. Ta na fama da wani rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Buchanan da abokin aikinta Poul Thisted, wanda dan kasar Denmark ne, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da su na tsawon watanni uku a yankin tsakiyar Somaliya. Da daren jiya Laraba, dakarun musamman na Amurka tafe cikin jiragen sama masu saukar ungulu sun sauka cikin wani sansanin soji da ke arewa maso yammacin birnin Mogadishu sannan su ka tinkari masu garkuwa da mutanen, su ka kashe a kalla 9 daga cikinsu.

Wani mai magana da yawun Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ya ce dakarun sun je ne da shirin kama masu garkuwan to amman ba su sami sukunin yin hakan ba.

Da ya ke bayyana aikin ceton, Shugaba Barack Obama ya ce Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin tabbatar da lafiyar ‘yan kasar da kuma hukunta wadanda su ka nemi cutar da su.

A wani shirin labarai na safiyar jiya Laraba, Mataimakin Shugaban Kasa Joseph Biden ya jinjina wa dakarun da su ka gudanar da aikin ceton.

Ya ce an auna lokacin kai daukin ne bisa la’akari da wasu dalilan da su ka hada da yanayin lafiyar wadanda aka yi garkuwa da su din.

XS
SM
MD
LG