Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Garin Tsagem, Jihar Katsina


Gidan rediyon Vision FM Katsina ya jagoranci shirin Da Dan Gari na wannan makon inda ya kai ziyara garin Tsagem da ke karamar hukumar Mani a jihar Katsina don jin tarihin garin.

Garin Tsagem ya shahara sosai kuma gari ne na Fulani da Malamai. Basaraken garin Buhari Usman, ya ce garin ya shahara a fannin kiwo da noma kuma har yanzu kaburburan sarakunan garin na baya na nan a wurin Dutsen Gandu, a cewar basaraken.

Duk da shahararsa, garin na fuskantar kalubalen karancin samun ci gaba, musamman ta bangaren hanyoyi da kuma karancin ruwa.

Saurari cikakken shirin wanda Abdul Jani ya gabatar.

Da Dan Gari: Tarihin Garin Tsagem, Jihar Katsina
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:32 0:00


Dubi ra’ayoyi

XS
SM
MD
LG