Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske Gwamnonin APC Zasu Kauracewa Taron Kasa?


Tambarin APC

Tun da shugaban Najeriya ya sanrda shirin yin taron kasa ake kai ruwa rana. Jam'iyyar APC ta ce wata dabara ce na karkata hankalin 'yan Najeriya daga matsalolin kasar.

Tun da shugaba Jonathan ya sanarda kafa wani kwamiti da zai shirya taron kasa jam'iyyar adawa ta APC ta ce wata dabara ce dake da wata manufa daban. To ko gwamnoninta su goma sha daya zasu amince da taron? Tambayae ce dake bukatar amsa daga garesu.

Muryar Amurka ta nemi ta san inda jam'iyyar ta tsaya. Abokin aiki Aliyu Mustapha ya zanta da Sanato Lawal jigo a cikin jam'iyyar wanda ya ce su basu ce zasu kauracewa taron ba idan da kyakyawar niya aka shirya shi kuma ita gwamnatin tarayya da gaske ta keyi ba wai akwai wani abu daga baya ba. Manufa a nan itace an kawo batun taron ne domin a kawair da hankulan mutane daga kasawar gwamnati kamar harkar ilimi da yanzu in ji shi ta sukurkuce gaba daya. Ga kuma uwa uba, batun tabarbarewar tsaro.

Tamkar taron bashi da ma'ana domin gwamnati ta ce za'a mikawa majalisar tarayya sakamakon taron. To in haka ne me ya hana gwamnati barin majalisar ta fada ma kasar matsalarta. Amma ita jam'iyyar APC dama can ta shirya ta yi taron kasa a watan Nuwamba wanda zai duba irin halin da kasar ke ciki da inda ya kamata ta sa gaba.

Ga karin bayani


please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai TsayeLABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG