Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske Ne Shekau Yana So Ya Mika Wuya?


Jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau
Jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau

A ‘yan kwanakin nan ana ta rade-radin cewa jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau yana so ya mika wuya ga mahukuntan Najeriya.

A lokacin da Babban jami’in cibiyar samar da bayanai a hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ke tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, ya ce “muddin Shekau ya bi tsarin da ake bi a kasar nan wajen mika wuya, toh, tabbas za mu karbe shi.”

Shi ma kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sagir Musa ya tabbatar da jin wannan jita-jitar.

“Muna da labarin cewa Shekau yana so ya mika wuya, amma wannan ba shi ke gabanmu ba, yakin da muke yi shi ya dame mu,” a cewar kakakin.

Sai dai tun da aka fara yada wannan jita-jitar mutane suka fara saka alamar tambaya kan lamarin.

Mai bincike kan kungiyar ta Boko Haram, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce “gaskiya tun da na karanta labarin a shafin Vanguard ban yarda da shi ba, a gani na, wannan maganar daga wajen jami’an tsaro ko kuma kawayenta ya fito.”

“Dalilina shi ne, saboda ainihin labarin da aka ruwaito, yana cike da kafafen da idan ka yi bincike za ka gane cewa suna matukar yaba wa sojoji ne.”

“Tun lokacin da aka fitar da labarin cewa sojojin Chadi sun yi nasara kan wasu mayakan Boko Haram a cikin kwanakin baya, na fara ganin karuwar labaran nasarorin sojojin Najeriya.”

A karshe ya jaddada yadda aka dawo da yawan watsa hotunan da aka jima da dauka, amma sai a wallafa su a matsayin wanda aka dauka yanzu “domin a nuna wa mutane cewa sojojin na fin karfin mayakan.”

An dai shafe akalla shekara 12 yanzu sojojin Najeriya da kasashen kewayenta, suna kokarin dakile kungiyar ta Boko Haram.

Tun da kungiyar ta fara kai hare-hare, ta kashe akalla mutum 18,000 da kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG