Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Halama Amurkawa Ne Su Ka Mutu A Hatsarin Jirgin Saman Afghanistan


kananan jiragen saman yaki masu saukar ungulu, samfurin Black Hawk irin wanda ya yi hatsari a kudu maso yammacin kasar Afghanistan dauke da sojojin Amurka

An yi amanna duka sojojin hudu sun mutu cikin hatsarin karamin jirgin saman yakin mai saukar ungulu

Jami’an gwamnatin kasar Amurka su fada a yau Jumma’a cewa mutane hudun da ke cikin karamin jirgin yakin Amurka mai saukar ungulun da ya fadi a kudu maso yammacin Afghanistan, dukan su Amurkawa ne da alama.

Jami’an soji sun ce an yi amanna cewa dukan su hudun sun mutu cikin hatsarin jirgin na jiya Alhamis cikin rashin kyawon yanayi.

Jami’ai sun ce a lardin Helmand jirgin saman ya fadi, kuma tunga ce ta ‘yan Taliban.

Kakakin kungiyar kawancen tsaro ta NATO Laftana-Kwamanda James Williams ya fadawa Muryar Amurka cewa akwai shakkun cewa, abokan gaba ne su ka kakkabo jirgin saman da harbi, amma ya ce ana gudanar da bincike akan musababbin faduwar jirgin saman.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya ce ya yi kyamar hotunan da sojojin Amurka su ka dauka tare da gawarwakin ‘yan tawaye, kuma ya ce hotunan sun kara jaddada bukatar cewa sojojin kasashen waje su fice daga kasar Afghanistan cikin gaggawa.

A cikin wata sanarwar da ya gabatar a jiya Alhamis shugaba Karzai ya fada cewa gaggauta ficewar sojojin kasashen waje da kuma daukan cikakkaen matakin mika ayyukan tsaro a hannun sojojin kasar Afghanistan, su ne kadai hanyar kawo karshen irin wadannan abubuwa masu sa ciwon rai.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG