Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Noma Aka Gina Najeriya- Masani


FILE - A farmer plows the field in Saulawa village, on the outskirts of Nigeria's north-central state of Kaduna.
FILE - A farmer plows the field in Saulawa village, on the outskirts of Nigeria's north-central state of Kaduna.

Masana Najeriya na kira ga gwamnati da al’umar kasar da su koma harkar noma domin a ciyar da kasar gaba ganin cewa da kudaden noma aka gina Najeriya ta kai matsayinta na farko a idon duniya.

A cewar tsohon shugaban hukumar hadahadar kasuwanci ta Chambers of Commerce, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, an gina Najeriya ne da albarkatun noma.

“Najeriya da ta dogara ne da noma da sana’oin hannu, da kudin fata da na kirgi da na gyada da na auduga da na ridi da na cocoa hatta kudin da aka hako mai da kudin wadannan noma aka yi amfani.” In ji Dayyabu a wata hira da ya yi da Sasshen Hausa na Muryar Amurka.

A cewarsa yanzu ya rage ne ‘yan Najeriya su koma ga Allah su zabo shugabanni na gari domin a fitar da kitse daga wuta.

“Kuma Allah da ikonsa sai ya kawo wanda ya ke da zafin da kimar da kuma kokarin ya ga ya yi wadannan abubuwan, amma kuma shi ba dan siyasa ba ne kuma ya kasa tunanin yadda zai janyo ‘yan siyasa a jikinsa ta yadda za su rinka tunatar da shi kan abubuwa.” Ya kara da cewa.

Muryar Amurka ta kuma tambayi Alhaji Dayyabu, ko guguwar canjin da ta kada a Najeriay za ta samar da shugabannin na gari?

Domin jin amsar wannan tambaya, saurari karashen hirar da su ka yi da Grace Alheri Abdu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG