Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dadadden Mataimakin Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Ya Kamu Da Cutar Corona


James Wani Igga

Dadadden Mataimakin Sudan Ta Kudu ya kamu da cutar coronavirus. James Wani Igga ya fadi ta kafar yada labaran Sudan Ta Kudu (SSBC) cewa sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ya kamu da cutar.

“An dau samfur daga jiki na don gwaji cikin ‘yan kwanakin da su ka gabata kuma a yau an gano cewa ina da cutar corona. Saboda haka, ina mai kira ga dukkannin ‘yan Sudan Ta Kudu cewa lallai fa su je a gwada su. Wannan na da matukar muhimmanci saboda mu tsai da yaduwar wannan annobar zuwa ga sauran mutane,” a cewar Igga.(Aikin tsaftace

A member of South Sudanese Ministry of Health's Rapid Response Team take a sample from a man who has recently been in contact with a confirmed case of the COVID-19 coronavirus in Juba, South Sudan on April 13, 2020. - Four cases of the COVID-19…
A member of South Sudanese Ministry of Health's Rapid Response Team take a sample from a man who has recently been in contact with a confirmed case of the COVID-19 coronavirus in Juba, South Sudan on April 13, 2020. - Four cases of the COVID-19…

(Aikin gwajin corona a Sudan Ta Kudu)

Igga ne babban jami’in Sudan Ta Kudu na biyar da ya kamu da cutar ta COVID-19, ya kuma fito fili ya fada.

Sabon ciyaman din na Kwamitin Yaki Da Cutar COVID-19 na kasa kuma Mataimakin Shugaban kasa na biyar, Hussein Abdelbagi ya kamu da cutar ta corona ne a makon jiya.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG