Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Ina Giwayen Da Suka Bayyana a Kebbi Suka Fito?


Wasu giwaye suna kiwo a kasar Gabon
Wasu giwaye suna kiwo a kasar Gabon

Rahotanni sun ce ta iya yiwuwa ruwan saman da aka yi ta tafkawa a 'yan kwanakin nan ne ya tilastawa giwayen suka yi kaura daga asalin yankunansu.

Wasu giwaye da ake kyautata zaton batan kai suka yi, sun bayyana a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mazauna yankin Zaria Kala-Kala a karamar hukumar Koko-Besse, sun ce sun wayi gari ne suka ga wasu giwaye uku a yankin suna kiwo.

Giwayen sun bayyana ne a karshen watan Agustan da ya gabata, lamarin da gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar a shafinsa na Twitter.

“A yau, wasu giwaye uku sun bayyana a karamar hukumar Koko-Besse a jihar Kebbi.” Inji Bagudu

Ya kara da cewa, “za a ba wadannan dabbobin da ba a saba ganin su ba kariya, kafin a mika su ga hukumomin da suka dace.”

Bayanai sun yi nuni da cewa ta iya yiwuwa daga dazukan Jamhuriyar Nijar da Benin giwayen suka fito.

Giwaye, ba dabbobi ba ne da ake samu a yankin na jihar ta Kebbi

Rahotanni sun ce ta iya yiwuwa ruwan saman da aka yi ta tafkawa a 'yan kwanakin nan ne ya tilastawa giwayen suka yi kaura daga asalin yankunansu.

A farkon watan nan, mazauna yankin na karamar hukumar ta Koko-Besse sun kai korafin cewa giwayen suna bata masu gonaki.

Amma a wani mataki na kaucewa kai hari kan giwayen, hukumomin sun rarrashe su tare da tabbatar masu da cewa za a biya su diyyar barnar da giwayen suka yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG