Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Yanzu Sai An Gwada Lafiyar Mutum Kafin A Yi Masa Rigakafin Korona - NAFDAC


NAFDAC
NAFDAC

Hukumar kula da sahihancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC, ta bayyana cewa, daga yanzu jami’an kiwon lafiya za su rika gudanar da gwaji kan yanayin lafiyar mutum kafin yi masa allurar rigakafin cutar korona birus a kasar.

Hukumar ta NAFDAC ta sanar da hakan ne biyo bayan lura da wasu illoli da alluran riga kafin suke haifarwa ga wasu 'yan kasar, wadanda kuma za'a iya kauce musu idan aka gudanar da binciken lafiyan mutum kafin ba da rigakafin.

NAFDAC ta kuma ce ta amince da karin alluran rigakafin cutar korona birus guda uku da suka hada da Moderna, Sputnik, Astrazeneca don amfani a Najeriya.

Hakan na zuwa ne gabanin isowar karin alluran rigakafin a Najeriya, biyo bayan shawarar da kwamitin ta na rigakafin ya bayar, tare da umarnin a yi amfani da rigakafin Moderna wanda aka sarrafa a kamfanin Pharma Madrid na kasar Sifaniya.

Sai kuma AstraZeneca kirar AZD1222 na kamfanin Bioscience na kasar Koriya ta Kudu da kuma Sputnik V na cibiyar Gamaleya da ke nazari kan ilimin cututtuka da kananan hallitu ta kasar Rasha don amfanin gaggawa.

Idan ana iya tunawa, hukumar NAFDAC ta ba da izinin gaggawa na yin amfani da alluran rigakafin Astrazeneca daga kasar Indiya, da Pfizer na kafmanin Bio-N-Tech da Jassen na Johnson da Johnson suka turo a Najeriya don yaki da cutar ta korona birus.

A ranar Alhamis ne, babbar daraktar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana wa manema labarai cewa NAFDAC ce hukumar kasa ta farko a nahiyar Afurka da ke da tsarin shiryawa dokoki don ba da iznin gaggawa idan bukatar hakan ta taso, musamman ba da damar yin amfani da allurar rigakafin cutar Covid-19.

Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugabar Hukumar NAFDAC
Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugabar Hukumar NAFDAC

Farfesa Mojisola ta kara da cewa, NAFDAC ta sanar da matsayar amincewa da amfani da rigakafan Moderna da AstraZeneca sai kuma Sputnik V da sharadi.

Ta ce hukumar ta bi matakan bincike da tantancewa kan dukannin alluran rigakafin, ta kuma gano suna da inganci, tare da gano amfanin su ya fi karfin illar da zasu iya haifarwa.

Kwamitin rigakafin hukumar dai ya kwashe akalla kwanaki 15 wajen yin nazari kan kunshin maganin rigakafin don tabbatar da cewa alfanun rigakafin ya fi illar ta yawa.

A ko wace illa da aka fuskanta kuma, jami’an hukumar da ma na lafiya matakin farko za su rika bin diddigi domin sa ido da daukar mataki idan bukatar hakan ta taso.

XS
SM
MD
LG