Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dage Zaben Gwamnoni A Najeriya Ne Dalilin Da Ya Sa Aka Dage Kidayar Jama’a – Garba Shehu


Hukumar Kidaya ta kasa
Hukumar Kidaya ta kasa

Majalisar zartarwar Nigeria a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da bukatar dage ranar fara aikin kidayar jama’a da gidaje a kasar. Malam Garba Shehu, babban jami’in yada labarai a fadar shugaban Najeriya ya yi karin bayani kan hujjar canza ranar fara wannan aiki.

Bayan da hukumar INEC ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha zuwa 18 ga watan Maris, hukumar kidayar kasa ta nemi gwamnati ta ba ta damar dage kidayar jama’a da gidaje daga ranar 29 ga watan Maris zuwa karshen watan Mayu, a cewar Garba Shehu.

Malam Garba Shehu ya kuma ce majalisar kolin kasar ta amince a ba hukumar kidaya ta kasa makudan kudi, da za a yi amfani da su don sayen wata na’ura da zata taimaka wajen yin kidayar.

Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)

Wannan dai shi ne karon farko da za a yi kidaya da fasahar zamani a Najeriya, a cewar Garba Shehu. Ya kara da cewa jami’ai zasu yi amfani da kwamfuta, sannan na’urar zata yi amfani da tauraron dan adam.

A kidayar da aka yi a shekarun baya, an samu korafe-korafe game da sakamakon kidayar, amma a wannan karon ana sa ran sabuwar fasahar zata taimaka wajen kawar da wadannan korafe-korafen.

Masu sa ido na hukumar kidayar jama'a wajen biyan albashi
Masu sa ido na hukumar kidayar jama'a wajen biyan albashi

Garba Shehu ya kuma ce a wannan tsarin, gwamnatin Buhari ba ta bada damar wani yayi amfani da kididdigar ya tada hankali ko kawo wani bambancin kabilanci ko na addini ba.

Nan take dai shugabannin hukumar gudanar da kidaya a karkashin jagorancin Malam Nasiru Isah Kwara, ba su ce komai ba akan batun, sai dai suka ce suna jiran karin bayanai daga fadar shugaban kasa.

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG