Dakarun Amurka sun ce sun kai hare-haren jiragen sama a Somaliya har sau shida, a ranakun Asabar da Lahadi, a yankin gabar ruwa da ke Gandarshe, inda su ka kashe mayakan al-Shabab 62.
Bataliyar sojin Amurka ta shiyyar Afirka, ta fada a wata rubutacciyar sanarwa cewa ta kai hare-hare sau hudu shekaran jiya Asabar, inda ta kashe mayakan al-Shabab 34. Ta ce wasu karin hare-hare biyu kuma da ta kai jiya Lahadi sun yi sanadin mutuwar mayaka 28.
Ita ma hadakar sojojin Afirka ta 'Africom' ta ce, "Mu, Bataliyar sojojin Afirka da abokanmu na Somaliya, mun kaddamar da wadannan hare-haren jiragen sama ne da zummar hana 'yan ta'adda amfani da wuraren da ke lunguna a matsayin mafaka, da kuma wuraren shirya ta'asarsu, da wuraren tsarawa da kuma binciken kan yiwuwar kai hare-hare na gaba."
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 30, 2023
Kamala Harris Ta Gana Da Mata ‘Yan Kasuwa Na Kasar Ghana
-
Maris 29, 2023
Zimbabwe Na Duba Yiwuwar Soke Hukuncin Kisa
-
Maris 29, 2023
Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.
Facebook Forum