Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Amurka Sun Kashe 'Yan Kungiyar Al-Shabab 6 a Somalia


Wannan ne karo na 12 da dakarun suka kai hari ta sama akan kungiyar mayakan dake Somalia.

Wani hari ta sama da Amurka ta kai yau Laraba ya kashe akalla ‘yan kungiyar al-Shabab 6 a kudancin Somalia, a cewar wata sanarwa da rundunar sojan Amurka ta fitar.

Harin ya faru ne kimanin kilomita 260 da kudancin Mogadishu, babban birnin kasar, a cewar sanarwa da rundunar rundunar sojan Amurka a Afrika ta fidda, duk da dai ba a bada karin bayani ba.

Hare-haren ta sama guda 3 da aka kai” an kaddamar da su ne tare da hadin guywar gwamnatin tarayyar Somalia, a cewar sanarwar.

Harin da aka kai yau Laraba shine hari na 12 da aka sanar wanda dakarun Amurka suka kai akan ‘yan kungiyar masu alaka da al-Qaida a Somalia tun daga ranar 1 ga watan Yuli.

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG