Accessibility links

Dakarun Amurka sun isa Uganda domin taimakawa a yaki mayakan kungiyar LRA


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama zai tura sojojin Amurka dari zuwa Afrika ta tsakiya domin mara bayan yunkurin yankin na shawo kan kungiyoyin mayakan sari ka noke dake gallazawa farin kaya.

Shugaban Amurka Barack Obama zai tura sojojin Amurka dari zuwa Afrika ta tsakiya domin mara bayan yunkurin yankin na shawo kan kungiyoyin mayakan sari ka noke dake gallazawa farin kaya.

Ana zargin ‘yan tawayen Ugandan Lord’s Resistence Army, karkashin jagorancin Joseph Kony da sace kananan yara da kisan kai da kuma fyade a Uganda da kuma wadansu kasashe dake makwabta.

Shugaba Obama ya shaidawa majalisa a cikin wata wasika da ya rubuta cewa, ya bada izinin tura dakarun Amurka yankin domin taimakawa wajen kawar da Kony daga bakin daga. Yace dakarun Amurka ba zasu yi fito mu gama da mayakan kai tsaye ba, sai dai kare kansu idan ta kama.

Rukunin dakarun Amurka na farko daga cikin sojoji 100 ya isa Uganda ranar Laraba.

Dakarun Amurkan zasu taimaka wajen samar da bayanai, da shawarwari da kuma tallafi a Uganda da Sudan ta Kudu, da jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Damokaradiyar jamhuriyar Congo.

Ana zargin kungiyar ‘yan tawaye ta Lord’s Resistence Army da kisa da garkuwa da jama’a da kuma yiwa dubun dubatan mutane kisan gilla a duk fadin Afrika ta tsakiya a wani kamfe da aka fara karshen shekara ta dubu da dari tara da tamanin. Kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa ta bada takardar sammace kan Kony, wanda take tuhuma da aikata laifukan yaki da gasawa bil’adama akuba.

XS
SM
MD
LG