Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Da Ke Biyayya Ga Gaddafi Sun Danna Sashen Birnin Benghazi


Wasu 'yan tawayen Libya kenan ke gudu lokacin da wani jirgin Libiya ya sako bam a inda su ke.

Dakarun da ke biyayya ga Shugaban Libiya Muammar Gaddafi a sun sake kaddamar da harin jiragen sama kan garin Ajdabiya da kafin nan ke karkashin ikon ‘yan tawaye, kuma har sun yi nasarar korar 'yan tawayen, wanda hakan ya basu damar kara dosar babbar cibiyar ‘yan tawayen wato birnin Benghazi.

Dakarun da ke biyayya ga Shugaban Libiya Muammar Gaddafi a sun sake kaddamar da harin jiragen sama kan garin Ajdabiya da kafin nan ke karkashin ikon ‘yan tawaye, kuma har sun yi nasarar korar 'yan tawayen, wanda hakan ya basu damar kara dosar babbar cibiyar ‘yan tawayen wato birnin Benghazi.

Shaidun gani da ido sun fadi yau Talata cewa hare-haren jiragen yaki sun galabaitar bayan birnin daga bangaren yammacin. Kamfanin dillancin labaran Faransa y ace an kashe a kalla wani sojan ‘yan tawaye daya.

Dakarun da ke biyayya ga Gaddafi sun jefa bama-bamai kan Ajdabiyya jiya Litini a lokaci gida kuma sun yi ta auna garin Zuwarah da ke gabar yamma, da ked a nisan kilomita 120 daga yammacin birnin Trabulus. Zuwarah dai na daya daga cikin karuruwan da ke yamma da ‘yan tawayen su ka kama lokacin zanga-zangar kin gwamnati wata guda day a gabata.

A halin da ake ciki kuma ba a san ko wane bangare ba ne ke rike da Brega mai tashar mai. Wani rahoto na yammacin jiya Litini y ace ‘yan tawaye sun sake kame ciki garin, a sa’ilinda kuma dakarun da ke biyayya ga Gaddfi ke iko da tashoshin.

A halin da ake ciki kuma Ministan Harkokin Wajen Faransa ya ce har yanzu kasarsa bat a gamsar da kawayenta kasashe takwas bas u goyi bayanta wajen hana jirage shawagi a wasu sassan Libiya a yinkurin hana jiragen yakin Libiya kai hari.

Ministan Harkokin wajen na Faransa Alain Juppe ya yi wannan jawabin ne ga gidan rediyonb Europe 1 a yau Litini. Manyan jami’an difflomasiyya daga manyan kasashe masu masana’antu sun taru a birnin Paris tun jiya Litini don tattauna irin matakin da yakamata su dauka kan rikicin Libiya.

Kasashen Takwas din sun hada da Amurka, da Rasha da Jamus da Faransa da Italiya da Burtaniya da Canada da Japan.

Da Faransa da Burtaniya na kan gaba wajen kiraye-kirayen a hana jirage shawagi a wasu sassan Libiya kuma sun garzaya Majalisar Din kin Duniya don neman goyon baya. Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya y ace dole ne a amsa wasu tambayoyi kafin a hana jirage shawagi a wasu sassan Libiya. To saidai bai kawar da yiwuwar nan gaba Rasha ta amince da kafa dokar hana jiragen shawagi ba.

XS
SM
MD
LG