Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Hadin Kan Afirka Zasu Fatattaki Mayakan al-Shabab daga Somalia


Dakarun hadin kan Afirka, AU, a Somalia
Dakarun hadin kan Afirka, AU, a Somalia

Dakarun kungiyar tarayyar Afirka ta AU sun kaddamar da wani shiri a kasar Somalia da zai fatattaki mayakan kungiyar al-Shabab daga yankin Shabelle, a kuma killace hanyar shigar da kayayyaki zuwa yankin.

Shaidu sun fadawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, sun ga sojojin kungiyar AU akan hanya da kuma wani yanki da ake noma tsakanin garin Afgoye da Bal’ad, sun kuma lura da cewa babu ‘yan kungiyar al-Shabab dayawa a yankin jiya Litinin.

Aikin da kungiyar tarayyar Afirka ke yi a Somaliya, da ake kira AMISOM, a wata sanarwa an fadi cewa an kaddamar da shi ne bayan da aka samu bayanai kan cewa kungiyar Al-Shabab na kawo rashin kwanciyar hankali a babbar hanyar da ta hada Mogadishu da filin saukar jiragen sama na Ballidogle, mai tazarar kilomita 90 arewa da babban birnin tarayya.

Ballidogle dai filin jiragen saman sojoji ne dake yankin Shabelle, inda dakarun Amurka ke horas da sojojin Somaliya.

Babu tabbacin ko harin da aka kai na jiya kan mayakan al-Shabab na wani bangare na zafafa hare-haren da sojojin Somali da na AU suke yi, amma shirin AMISOM yace shiri ne kan mayakan al-Shabab, kuma za a gudanar da shi sannu a hankali.

Shekaru biyu kenan tunda kungiyar AU ta kaddamar da hari kan kungiyar Al-Shabab.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG