Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraqi Sun Shiga Birnin Fallujah


Mayakan Shiya kusa da Fallujah

Birnin Fallujah ya yi shekara biyu a hannun mayakan ISIS kafin makonni uku da suka gabata dakarun Iraqi da wasu dakarun wasu kungiyoyi tare da goyon bayan Amurka suka farma kewayen birnin da zummar shiga birnin daga wurare daban daban

A Iraqi dakarun kasar sun shiga birnin Fallujah, mako uku bayanda suka kaddamar da farmaki da niyyar sake kwato birnin dake hanun mayakan sakan Daesh ko ISIS, kamar yadda wani kakakin rundunar tsaron taron dangi da take fafatawa da ISIS a Iraqi da Syria Kanal Chris Garver, ya gayawa manema labarai da suke aiki daga ma'aikatar tsaron Amurka ,wato, Pentagon ta wayar celula jiya Laraba daga Bagadaza.

Wannan farmaki yana zuwa ne a kuma dai dai lokacinda wasu rundunonin tsaron kasar, rundunar 'Yansanda a Iraqi, mayakan sakai na kabilu da suke yankin Anbar, da sauran wasu kungiyoyin mayaka suke ci gaba da yiwa birnin Fallujah zobe, domin hana mayakan Daesh turo karin mayakan sakai, ko samar musu da kayan yaki.

Mayakan kungiyar Daesh ko ISIS, suna rike da wannan birni kusan shekaru biyu ke nan yanzu.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG