Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Iraqi Sun Bude Wata Hanyar da Wasu Mazauna Fallujah Zasu Fice


Firayim Ministan Iraq Haider al-Abadi yayinda ya ziyarci mayakan kasar a bakin daga
Firayim Ministan Iraq Haider al-Abadi yayinda ya ziyarci mayakan kasar a bakin daga

A Iraqi wani Janar na rundunar mayakan kasar da suke ci gaba da yunkurin sake kwato birnin Fallujah dake zaman wata babbar tunga ga mayakan sakan ISIS,sun bude wata dama, wacce masu aikin ayyukan jinkai suka ce ta baiwa mazauna birnin kusan dubu 4 tserewa daga birnin cikin kwanaki uku da suka wuce.

Majalisar kula da 'yan gudun hijira mai cibiya a Norwa ta yaba da wannan kafar da aka tabbatar da ita ranar Asabar, a dai dai lokacinda ma'aikata da suke aiki karkashinta suke fadi tashin ganin sun samar da kulawa ga sabbin 'yan gudun hijirar.

Kakakin kungiyar Karl Schembri,ya bayyana murnarsa, duk da haka yayi gargadin cewa za'a fuskanci karancin kayayyaki kamar ruwan sha saboda karin 'yan gudun hijira. Yace "muna tsammanin wasu dubban mutane zasu fito cvikin 'yan kwanaki masu zuwa." Ya gayawa manema labarai.

Janar Yahya Rasool, yace sun bude hanyar ce, bayan da suka kori mayakan sakai daga wata gunduma dake dab da kan gabar kogin Euphrates.

Makon jiya, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan makomar kimanin farar hula dubu 90 wadanda aka haikaknce sun makale cikin birnin ba tareda abinci ko kiwon lafiya ba.

XS
SM
MD
LG