Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Isra’ila Sun Bakuci Mutane Su Fice Daga Wasu Garuruwan Lebanon


Wani yankin Lebanon da Isra'ila ta kai hari
Wani yankin Lebanon da Isra'ila ta kai hari

Rundunar ta IDF ta fada a ranar Alhamis cewa, wani harin da Isra’ila ta kai da jiragen yakinta ya kashe wani kwamandan Hezbollah Khader Al-Shahabiya.

Sojojin Isra'ila sun yi wa mazauna garuruwa da kauyukan kudancin Lebanon kashedi a ranar alkhamis da su yi maza su fice daga gidajen su, su koma yankin arewa domin kada wani abu ya same su yayin da Isra'ilar take ci gaba da kai farmaki ta kasa akan Hezbollah.

A shafin sada zumunta na manhajjar X, mai magana da yawun dakarun tsaron Isra’ila na IDF cikin harshen larabci, laftanar kanar Avochay Adraee ya gargadi mazauna yankuna da su koma yankin Arewa da kogin Awali domin su tsira da ransu." Ya yi gargadin cewa duk wani yunkurin kutsawa kudu zai zama da hadari.

Dakarun Isra’ila sun saki wani faifayin bidiyo da yayi ikirarin cewa dakarun su ne a sa'adda suka kai farmaki kudancin Lebanon inda suka kai samame akan wasu da zummar dakilewa da lalata kayan cibiyoyin kungiyar mayakan Hezbollah, kamar yadda suka sheda a cikin wata sanarwar.

Rundunar ta IDF ta fada a ranar Alkhamis cewa, wani harin da Isra’ila ta kai da jiragen yakinta ya kashe wani kwamandan Hezbollah Khader Al-Shahabiya.

Jami’an lafiyar Lebanon sun fada a ranar alkhamis cewa wani harin saman da Isra’ila ta kai ya fada wani gida inda mutane suke zama a Beirut, inda ya kashe mutane 6 sannan ya jikkata wasu mutane bakwai.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG