Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Na Ci Gaba Da Kai Farmaki Kan Boko Haram A Dajin Sambisa


Jirgin Saman Yakin Najeriya Kirar Alpha-Jet
Jirgin Saman Yakin Najeriya Kirar Alpha-Jet

Sojojin saman Najeriya da na kasa na ci gaba da farautar burbudin 'yan Boko Haram dake kokarin sake mamaye dajin Sambisa inda suke da gine gine a karkashin kasa masu mahimmanci garesu

Kakakin hedkwatar sojojin saman Najeriya dake fafatawa da kungiyar Boko Haram a jihar Borno, Air Vice Marshall Adetokunbo Adesanya ya yi bayani dangane da tsananta hare-haren da suke kaiwa yanzu kan burbushin 'yan ta'addar.

A cewarsa mayakan sama da sojojin kasa dake cikin dakarun Operation Lafiya Dole, suna can suna barin wuta akan burbudin 'yan Boko Haram dake neman sake kafa sansanoni a cikin dajin Sambisa. Yace Njimi na daya daga cikin wuraren da suka hango Boko Haram na kokarin tattaruwa, suka kuma yi rugu-rugu da wurin.

Haka ma suka yi a wurin da ake kira Camp Zero. 'Yan Boko Haram da ba su mutu ba da suka fara tserewa bisa babura an yi ta kai musu hare-hare, aka kuma gama da su, in ji kakakin.

Kakakin ya kara da cewa 'yan Boko Haram din na kokarin sake taruwa wuri guda ne dalili ke nan da suke fakonsu su gama da su.

Aliko El-Rashid Harun wani tsohon hafsan rundunar sojojin saman Najeriya ya ce lokacin da aka kwato sashen dajin Sambisa bai kamata sojojin su bar wurin ba amma da suka watse suka bar wurin, sai 'yan ta'addar suka koma suka sake kafa gurbinsu. A cewarsa Camp Zero din na da muhimmanci a wurin 'yan Boko Haram saboda gidajen karkashin kasa dake wurin da wurare na musamman da suke yin horo dukkansu a cikin kasa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG