Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Kai Hari Kan Mayakan Boko Haram, ISWAP


Wani lokacin a can baya da dakarun Najeriya da takwarorinsu na Chadi suke atisaye kan yaki da kungiyar Boko Haram
Wani lokacin a can baya da dakarun Najeriya da takwarorinsu na Chadi suke atisaye kan yaki da kungiyar Boko Haram

Hare-haren biyu na zuwa ne kasa da makonni biyu da wnai harin Boko Haram da ya halaka mutum sama da 30 a wani gidan kallon kwallo a Maiduguri, sannan kasa da mako guda, bayan wani harin mayakan da halaka wasu dakarun Najeriyar.

A wasu samamen sama biyu da ta kai kan wasu tungar mayakan Boko Haram a yankunan Bakassi da Gobara da ke jihar Borno, rundunar dakarun saman Najeriya ta ce ta halaka mayaka da dama.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, an kaikaici yankin Gobara ne bayan da aka gano cewa mayakan na Boko Haram suna amfani da wurin domin boye makamai da yin wasu aikace-aikacensu.

Sanarwar wacce Daramola ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta hada da wani hoton bidiyo mai tsawon dakika 52 wanda ya nuna yadda aka kai hare-haren wadanda suka bata kayayyakin mayakan da kuma kashe da dama daga cikinsu.

Baya ga wannan hari, sanarwa ta ce wani hari na daban, ya kaikaici yankin Bakassi da ke gefen Tafkin Chadi a arewacin jihar ta Borno, inda aka far ma mayakan kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP,) inda a nan ma aka halaka mayaka da dama.

Hare-haren biyu an kai su ne a ranar 26 ga watan Yunin nan mai karewa.

Wadannan samame biyu na zuwa ne kasa da makonni biyu da wani harin Boko Haram da ya halaka mutum sama da 30 a wani gidan kallon kwallo, sannan kasa da mako guda, bayan wani harin mayakan da halaka wasu dakarun Najeriyar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG