Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko Haram


Dakarun Sojoji Najeriya masu sharar faggen yaki karkashin Rundunar lafiya dole, sun fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haran daga kauyen Chikun Gudu dake arewacin jihar Borno, a ranar juma’a

A fafatawar da akayi dakarun na Najeriya sun kashe ‘yan kungiyar da dama sun kuma kama goma sha hudu da rai inda wasu da dama suka tsere da raunukan harbi.

A cikin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da motoci biyu kirar Toyota da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka sato daga jami’an tsaron jamhuriyar Nijar, masu dauke da bindigogi, da kuma wasu motoci biyu kirar Toyota Hilux, da ‘yan kungiyar suka sato daga harabar “Task Force Battalion” na Sojojin Najeriya, da ingin din da ake sawa kwalekwale, da naurar lantarki mai amfani da hasken rana da jigidar albarushin da ake harbo jirgin sama.

Sauran sun hada da wasu safarin albarusai irin wanda kungiyar NATO, ke amfani dashi da Qur’anai da wasu litattafen addini da machine na hawa fiye da saba’in wanda duk aka konesu. An kuma gano wasu shaguna uku cike da magunguna na asibiti da wasu uku kuma cike da kayayyakin amfanin yau da kullum.

A wannan arangamar da akayi Sojojin Najeriya hudu sun sami raunuka kuma tuni aka kaisu asibiti inda ake yi masu magani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG