Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Syria Sun Yi Lugudan Wuta a Kan 'Yan tawaye


Sojoji da jami'an tsaro suke duba daya daga cikin ginin gwamnati da aka kaiwa hari a birnin Damascus kasar Syria.

Jiragen yakin Syria sun yi ruwan bama-bamai a Jisr al-Shughour dake arewa maso yammacin kasar a yau din nan lahadi. Kwana daya bayan kungiyar Nusra Front masu alaka da Al-Qaeda sun kwace garin a karo na farko a shekara hudu da ake yakin kasar.

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai shelkwata a Birtaniya da ke lura da yanayin yakin Syria, sun ce akalla an harba makamai hudu da suka ragargaji birnin, wanda shi ne ya ragewa gwamnati da take iko da shi a yankin Idlib.

Hakan na faruwa ne bayan da ‘yan tawaye suka kwace ikon babban birinin yankin Idlib wata guda da ya wuce.

Kwace garin Jisr al-Shughour mai kimanin mutane dubu 50 na daga cikin jerin biranen da Damascus ta rasa a arewa da Kudancin yankunan Syria.

Babu takamaiman rahoton wadanda suka mutu a harin na yau, amma kungiyar kare ‘yancin dan adam din ta ce akalla mutane 27 suka mutu a harin jiya asabar, ciki har da ‘yan tawayen.

Kafar yada labaran gwamnati ta ce sun fito da dakarunsu wajen Jisr al-Shughour domin gujewa ci gaba da raunata fararen hula.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG