Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Turkiyya Na Barin Wuta A Arewacin Syria


Sojojin Turkiyya kusa da garin Hassa dake kan iyaka da Syria
Sojojin Turkiyya kusa da garin Hassa dake kan iyaka da Syria

Yau Litinin dakarun Turkiyya suka soma barin wuta a yankin Afrin dake arewacin kasar Syria domin kare kauyukanta dake kan iyaka da kasar ta Syria daga hare haren 'yan ta'adda

Dakarun Turkiyya sun yi barin wuta kan arewacin Syria a yau Litinin, inda suka maida karfi wajen korar mayakan Kurdawa daga yankin Afrin, kuma jami’ai sunce za’a kammala wannan farmaki ba da dadewa ba.

Haka nan an samu rahoto cewa mayakan Kurdawan da aka sani da lakabin YPG sun gwabza da jami’an tsaron Turkiyya a arewa maso yammacin Afrin.

Mataimakin Firayim Ministan Turkiyya Mehmet Simsek ya ce matakin sojin zai taimaka wajen rage hare haren ta’addanci da ake kaiwa Turkiyya.

Hukumomin Turkiyya a Ankara suna zargin kungiyar YPG wacce take iko da Afrin cewa tana da alaka da wata kungiya ta masu tada kayar baya a cikin kasarta. Firayim Ministan Turkiyya Binali Yildrim ya ce makasudin wannan farmakin mai suna Olive Branch da turanci shine a samar da wuri a yanki mai girman kilomita 30 domin kare kauyukan Turkiyya daga hare hare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG