Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai Da Dama Na Iya Rasa Damar Rubuta Jarabawar JAMB Ta Bana A Najeriya


Hukumar Shirya Jarabawa ta JAMB
Hukumar Shirya Jarabawa ta JAMB

Ana fargabar cewa daliban Najeriya da dama ne ba za su sami damar rubuta jarabawar share fagen shiga jami'a ta JAMB ba a shekarar karatu ta 2021/2022, sakamakon dagewar da hukumar shirya jarabawar ta JAMB ta yi, na sanya lambar katin zama dan kasa wato NIN, a cikin sharudan yin rijistar jarabawar.

Hukumar shirya jarabawar ta share fagen shiga jami’a ta Najeriya, JAMB, ta soma sayar da takardun cikewa domin yin rijistar rubuta jarabawar UMTE da DE na bana.

To sai dai a ranar Alhamis da ta gabata, hukumar ta JAMB ta ba da sanarwar dage soma rijistar jarabawar ta bana, a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli a bangaren dalibai, bankuna da sauran takwarorin aikinta.

Rahotanni sun bayyana cewa dagewar ta zama wajibi ne sakamakon yadda dalibai da dama suka kasa kirkira rumbun bayanan su domin yin rijistar da aka shata gudanarwa daga ranar 8 ga watan Afrilu zuwa 15 ga watan Mayu.

Fabian Benjamin, Kakakin Hukumar JAMB
Fabian Benjamin, Kakakin Hukumar JAMB

Shugaban sashen watsa labarai na hukumar JAMB Fabian Benjamin ya fada a cikin sanarwar cewa “an sami tsaikon ne saboda wasu wasu matsaloli da suka bijiro, a kokarin sanya ka’idar amfani da lambar shaidar zama dan kasa, NIN, a sha’anin rijistar jarabawar.”

Benjami ya ce ana nan ana kokarin shawo kan matsalar, kuma da zarar an kammala, za’a ci gaba da aikin rijistar jarabawar.

Akan haka ya yi kira ga dalibai da su kara hakuri, a yayin da hukumar za ta ba da sanarwa idan ta kammala gyaraN, ta yadda dalibai za su ci gaba da yin rijistar.

Tun a bara ne hukumar ta JAMB ta kuduri aniyar tilasta amfani da lambar shaidar zama dan kasa (NIN) a rijistar rubuta jarabawar share fagen shiga jami’a ta UMTE/DE ta shekara ta 2020, to amma kuma ta janye kudurin sakamakon matsalolin da dalibai suke fuskanta wurin yin rijistar.

Dalibai Na Rubuta Jarabawar JAMB A Najeriya
Dalibai Na Rubuta Jarabawar JAMB A Najeriya

Masu ruwa da tsaki a lamarin da kuma musamman iyaye, sun yi kira ga hukumar ta JAMB, da ta dakartar da ka’idar ta sanya lambar NIN da kuma kirkira rumbun bayanai na dalibai, ta ba dalibai damar yin amfani da kowane irin katin SIM na salula mai rijista, domin yin dukkan lamurran da suka danganci rijistar jarabawar ta JAMB.

XS
SM
MD
LG