Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai, Iyaye Ba Su Yi Na'am Da Shawarar Trump Ta Ba Malamai Bindiga Ba


Shugaban Amurka Donald Trump yana ganawa da daliban sakandare da malamai da kuma iyaye da hare-haren ya taba shafa.

Dalibai, iyaye da malaman makaranta da suka halarci wani zama a Fadar gwamnatin Amurka ta White House, sun nuna adawarsu da shawarar da shugaba Trump ya bayar ta a rika ba malaman makarantar bindiga a aji, a wani mataki na shawo kan matsalar masu kai hare-hare a makarantu.

Shugaban Amurka ya yi karin haske kan shawarar da ya bayar ta cewa a samar wa malaman makaranta bindigogi da za su rika shiga da su ajujuwa a matsayin kariya.

Trump ya ce za a bai wa malaman da suke da kwarewa ne wajen sarrafa bindiga, wacce za ta kasance a boye a jikinsu.

Kwana guda bayan wata ganawa da shugaban ya yi mai sosa rai da daliban da suka tsira daga masu kai hare-hare a makarantu, da kuma iyaye, shugaba Trump, a wani sako da ya aika ta shafinsa na Twitter, ya ce “kashi 20 cikin 100 ne kadai cikin malamai, ke da kwarewar iya harbi, idan har wani mai tabin hankali ya zo da wani mugun nufi.”

A lokacin ganawar ta jiya ne, Trump ya ce, za a baza tsoffin dakarun kasar, a baki dayan makarantu wanda hakan “ka iya taimaka wa wajen samun mafita kan wannan matsala.

“Lallai za mu sa matakan cancantar mallakar bindiga, za kuma mu yi abubuwa da dama, babu haufi, za mu duba yiwuwar hakan.”

Shugaban na Amurka ya gana da mutanen ne a Fadarsa ta White House, inda har a wani lokacin ganawar, ya tambayi masu halartar taron ko sun yi na’am da shawararsa?

Sai dai mutane kadan ne suka daga hannayensu kan amincewar da shawarar, amma kuma a lokacin da ya tambayi wadanda shawarar ba ta kwanta musu ba, sai mutane da dama suka daga hannu da ke nuna adawa da shawarar.

An yi kiyasin mutane kusan 40 suka halarci zaman.

Mafi aksarin wadanda suka nuna adawarsu kan wannan shawarar ta Trump, dalibai ne da iyaye da kuma malaman da irin wannan hari na makaranta ya taba shafa.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG