Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaso 90 Cikin 100 Na Daliban Makarantar Kenya Sun Fadi Jarrabawa


Dalibai a Kenya
Dalibai a Kenya

'Yan majalisar adawar Kenya na kalubalantar gwamnati akan dalilin faduwar dalibai dayawa a jarrabar gama sakandare ta wannan shekarar.

Wasu Wakilan jam’iyya mai adawa a majalisar dokokin kenya suna kira da gwamnatin kasar da ta binciki dalilan da yasa kaso 90 cikin 100 na daliban da suka dauki jarrabawar gama sakandare a shekarar 2017 suka fadi, duk da cewa ministan ilimi na kasar ya nuna gamsuwarsa da sakamakon.

A yayin da yake wa manema labarai jawabi a birnin Nairobi, dan majalisa Caleb Amisi yace dole ne majalisar ta san dalilan da yasa kaso 10 ne kawai suka ci makin da zai basu damar shiga jami’a.

"Dole ne a umurci ma’aikatar jarrabawar kasar Kenya da ta bada bayanai akan wannan gagarumar faduwar haka kuma ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kanshi," a cewar Amisi. "Kuma kamfanin binciken da aka fi yarda dashi a Kenya ne ya kamata ya gudanar da wannan binciken."

Sakamakon ya haifar da damuwa ga iyayen daliban, malamai da ma sauran mutane saboda damuwa akan rayuwar daliban da kuma ingancin karatun Kasar ta Kenya.’

Babbar tambaya anan itace menene ya kawo faduwar? Laifin daliban ne ko kuwa malaman, jadawalin ko kuma saurin sakawa jarrabawar hannu da aka yi a cikin sati uku kawai?

Wani dan majalisar Mark Nyamita yace dole ne a gyara wannan matsalar ko kuma a haramtawa miliyoyin matasan Kenya shiga makarantun gaba da sakandare.

Ya kara da cewa “idan wannan abun ya ci gaba a wannan gwamnatin a shekaru biyar masu zuwa, zamu samu fiye da mutane miliiyan 2.5 wanda rayuwarsu ke cikin hadari”.

Ana ci gaba da kira ga gwamnatin tarrayyar da ta shirya taro na musamman domin duba lamarin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG