Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Liberia Suna Jiran Sakamakon Zabe


Takardun Zabe A Liberia
Takardun Zabe A Liberia

An gama kada kuriar masu neman kujerar shugaban kasa a Liberia, inda a halin yanzu 'yan kasar na sauraron wanda zai maye gurbin shugabar da ta yi mulki har na tsahon wa'adi buyi, duk da cewar mutane basu fita zaben yadda aka so ba.

A jiya Talata ne ‘yan kasar Laberiya suka kada kuri’ar zaben fidda gwani na shugaban kasar. Yanzu suna dakon sakamakon zaben, wanda ka iya kai ‘yan kwanaki kafin a fitar da shi.

Tsohon zakaran kwallon kafa George Weah, da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai, ne suka yi takarar domin maye gurbin shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf, bayan ta kammala wa’adi biyu a matsayin shugabar kasa, wanda dama kundin tsarin mulkin kasar ya amince da shi.

Jami’an zabe sun ce jama’ar da suka fita zaben ba su da yawa, ba su kai wadanda suka kada kuri’a a ranar 10 ga watan Oktoba ba, inda Boakai da Weah ke kan gaba, abinda ya sa suka kai ga zaben na fidda gwani.

Masu sa ido akan zaben sun ce an shirya mazabun fiye da yadda aka tsara su a zaben watan Oktoba, kuma ba a sami wasu matsaloli ba sosai. Hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta ce an gano wata mata data so ta kada kuri’a sau biyu, kuma tuni aka kamata.

Duka ‘yan takarar biyu, sun gudanar da yakin neman zaben su ne kan samar da ayyukan yi, ilimi, da samar da ababen more rayuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG