Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jami'o'in Gwamnatin Nijer Sun Shiga Yajin Daukar Darasi


A shekarar 2010, ne aka sami Karin jami’o’I uku mallakar gwamnati akan guda dayar da ake da ita a jamhuriyar Nijer, wato jami’ar Abdul Mumini ta Yamai kafin daga bisani hukumomin kasar su bada sanarwar kafa wasu sababbi a wasu jihohin kasar guda hudu domin rage cunkoson dalibai.

Sai dai tun ba’a je ko’ina ba wadannan jami’o’i sun fara fuskantar cikas saboda dalilai na rashin kudaden gudanarwa kamar yadda a jiya 1 ga watan satumba daukacin jami’oi mallakar gwamnatin kasar suka kammala babban hutu.

Daliban sun shiga yajin daukar darasi na tsawon kwanaki 3 domin tilastawa hukumomi biya masu wasu mahimman bukatu yayinda su ma malaman jami’oi suka yi barazanar dakatar da aiyukan koyarwa muddin ba a biya bashin albashin wasu takwarorinsu ba kafin ranar 8 ga watan satumban nan.

Wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa wannan yajin daukar darasi sun hada da rashin basu alawus alawus kamar yadda maga takardar kungiyar daliban jami’a wato Sallau Shi’abou ya bayyana.

Domin Karin bayani saurari rahoton Sule Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG