Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jami'ar Usman Dan Fodio Sun Yi Zanga Zanga

Daruruwan daliban jami'ar Usman Dan Fodio Sokoto suke zanga zanga.

Daruruwan daliban jami'ar Usman Dan Fodio ne suka yi zanga zanga kan kasawar gwamnatin tarayya ta sake gine gadar da ta hade jami'ar da sauran sassan jihar. Wacce ta kariye tun bara sakamakon ambaliyar ruwa.

Daliban wadanda suka yi zanga zangar a safiyar Juamma'a, sun ce rashin gyara gadar zai yi illa ga rayuwarsu da ma karatu da suke yi. Sun bayyana damuwarsu ce ganin daminar bana ta fara kankama.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi alkwarin gwamnatin tarayya zata sake gyara gadar lokacinda ya kai ziyarar jajantawa al'uma da kuma gwamnatinn jihar.

XS
SM
MD
LG