Accessibility links

An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Hedkwatar 'Yansandan Najeriya A Abuja


'yan kwana kwana suke koakrin kashe wutar da ta biyo bayan harin kunar bakin wake a hedkwatar 'yansanda a Abujan Najeriya.

Wani bam mai karfin gaske ya fashe a harabar hedkwatar rundunar ‘Yansandan Najeriya a Abuja, har ya kashe mutum daya.

An kai harin kunar bakin wake a harabar hedkwatar ‘Yansandan Najeriya a Abuja, har ya kashe mutum daya.

A hira da yayi da MA wani kakakin kungiyar Boko Haram yace kungiyar ce take da alhakin kai harin.

Jami’an hukumar agajin gaggawa sun ce suna jin dan harin kunar bakin wake ne ya kai harin kuma da alamun fashewar ta halaka shi.

A hira da yayi da Muriyar Amurka, wani kakakin kungiyar Boko Haram yace kungiyar ce take da alhakin kai harin.

Ana aza laifi jerin hare hare a arewa maso gabashin kasar kan kungiyar ta Boko Haram inda suke auna hare harensu kan ‘Yansanda, jami’an gwamnati, da kuma wasu fitattu.

Fashewar ta yau Alhamis ta auku ne cikin wani wurin adana motoci kusa da sakatariyat ta ‘Yansanda. Tashar talabijin ta NTA ta nuna hoton vidiyo da aka ga hayaki bakikkirin yana tashi daga motoci da harin ya lalata.

Tuni ‘yan kwana-kwana da masu agajin gaggawa suka isa wurin,kuma jami’an ‘Yansanda sun killace dukkan hanyoyi da zasu kai ind a aka kai harin.

Kamdfanin dillancin labaran Reuters, ya amabci wani jami’in kungiyar agaji ta Red Cross yana cewa suna dauke gawarwaki da jinyar wadanda suka jikkata.

Muna da karin bayani bayan labaran Duniya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG