Daliban suna kokarin ketara gadar dake tsakanin Jami'ar Abdulmummuni da bangaren hagu na birnin Yamai domin gabatar da koke-koke ga hukumomin mulkin soja game da matsanancin halin rayuwa da na karatu da suke ciki wasu sojoji suka harbesu ranar 9 ga watan Fabraairu na shekarar 1990.
Tun daga ranar da aka bindige daliban har yanzu ba'a gano jami'an tsaron da suka yi kisan ba dalili ke nan da daliban kasar Nijar ke fitowa kan tituna kowace ranar tara ga watan Fabrairu da zummar tunatar da gwamnatin kasar ta aiwatar da bincike domin a gurfanar da duk wanda yake da hannu a aika aikar.
Ko a wannan Alhamis wadda ita ce tara ga watan Fabrairu dubun dubatan dalibai suka fito domin tunawa da 'yanuwansu tare da kiran gwamnati ta yi masu adalci.
Sakataren kungiyar dalibai ta kasa Sumana Useni Sambo yace zasu cigaba da gwagwarmayar kwato hakkin dalibai daga hannun gwamnatin Nijar tare da cigaba da matsin lamba har sai an zakulo wadanda suka kashe 'yanuwansu shekaru 27 da suka gabata. Saboda haka ya kira daliban kasar su kara jan damara.
Baicin wannan gangamin daliban sun sha alwashin sake fitowa domin su tambayi gwamnatin inda ta sa gaba game da harkokin ilimi musamman na jami'a.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.