Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Sakkwaton Najeriya a Nijar Sun Ce Suna Jin Jiki


University Graduates

Wasu dalibai ‘yan asalin jihar Sokoto da gwamnati ta tura karatun jami’a a kasar Nijar, sun koka yadda suke kai ruwa rana kafin samun na masarufin da zasu kai baki.

A 'yan shekarun nan gwamnatocin jihohin Najeriya sun yi rubdugun kai wasu daliban jihohinsu zuwa karo ilimi a kasashen duniya bisa matakai daban-daban, a tsarin da suke ganin wata sila ce ta ciyar da al'ummar jihohinsu gaba bayan sun dawo. to amma yawanci daliban na ta kokawa da cewa ba a kula da su.

Daliban Najeriya da dama da ke karatu a kasashen waje bisa tallafin karatun gwamnati suna kokawa da cewa an kaisu an baro ba tare da ci gaba da kula da su yadda ya kamata ba.

Sai dai kuma wasu jami’an gwamnati yawanci suka musanta cewa daliban na shan wuyar da cewa wani lokaci kamar zuzutawa suke yi. Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya tuntubi daya daga jami’an gwamnati akan lamarin.

Inda ya nuna cewa har da gajen hakuri, domin kuwa ma wasu an biya musu kudaden shekaru daya zuwa biyu na zangon karatun da aka tura su yowa a kasashen.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG