Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibin Najeriya Ya Ja Hankalin Duniya Da Zanen Mahaifar Mace Bakar Fata


Lucy Mbewe, mai dauke da juna biyu a kasar Malawi. Mun yi amfani da wannan hoton ne domin nuna misalin mata masu dauke da juna biyu. 23 Mayu, 2021

Zanen Ibe na dauke ne da hoton mahaifar mace mai ciki kuma bakar fata- irin hoton da ba’a cika gani ba a zane-zanen sha'anin kiwon lafiya.

Wani dalibi mai karatun neman zama likita da har ila yau yake harkar zane-zane daga Najeriya, ya ja hankalin duniya kan yadda ake samun karancin wakilcin al’umomi daban-daban a litattafan aikin likitanci da ake wallafawa bayan da ya yi wani zane da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Chidiebere Ibe dan shekara 25 da haihuwa, yana shekarar shi ta farko a Jami’ar koyon likitanci a birnin Kyiv na kasar Ukraine.

Zanen Ibe na dauke ne da hoton mahaifar mace mai ciki kuma bakar fata- irin hoton da ba’a cika gani ba a zane-zanen fannin kiwon lafiya.

Wannan zane na ban mamaki na Ibe ya samu karbuwa da sauri, duba da yadda mafi yawan mutane suke lura da cewa yawancin zane-zanen da ake wallafawa a fannin kiwon lafiya yana bayyana mata fararen fata ne.

Tuni zanen na Ibe ya samu goyon baya daga masu amfani da kafafen sada zumunta inda ya samu fiye da 95,000 a shafinsa na Instagram- lamarin da dalibin ya ce bai taba tsammani ba.”

“Duk manufar ita ce, ci gaba da yin magana game da abin da nake sha’awa.” In ji Ibe.

Samun daidaito cikin harkar kiwon lafiya, sannan kuma mu nuna kyawun bakar fata, Ibe ya fada wa jaridar HuffPost Uk. “Ba wakilci irin wannan kadai muke bukata ba, muna bukatar karin mutane da zu su kirkiri wakilci kamar wannan.”

Daga cikin fitattun mutanen da suka yi tsokacin yabo kan wannan zane har da fitacciyar mai tallata kayan zamani a Amurka Naomi Campbell wacce ta rubuta "Mun gode."

Wani mai amfani da shafin Instagram kuma cewa ya yi, "ban taba ganin zane mai ban sha'awa irin wannan ba, ka ci gaba da wannan abu mai kyau da kake yi," kamar yadda jaridar ta HuffpostUK ta ruwaito.

Ibe dan asalin jihar Ebonyi ne a Najeriya, ya kuma koyi aikin zane-zane ne a lokacin da aka yi kullen Coronavirus. Kafar watsa labarai ta Artnet News ta bada rahoton cewa, yanzu haka Ibe shi ne babban jami’in zane-zanen harkokin kiwon lafiya, kuma darektan kirkire-kirkire na mujallar labarai akan tiyatar kwakwalwa ta duniya.

Bisa tarihi zane-zanen kiwon lafiya ya dade yana haska mata fararen fata zalla kuma har yanzu ana yi.

XS
SM
MD
LG