Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Ke Sa ‘Yan Siyasa Sauya Sheka


Wata ma'akaciyar Hukumar Zabe ta na aiki a rumfar zabe a Najeriya.
Wata ma'akaciyar Hukumar Zabe ta na aiki a rumfar zabe a Najeriya.

Batun canja sheka a Najeriya ya fara zama ruwan dare yayin da ake tunkarar zauban gwamnoni da za gudanar a karshen mako mai zuwa.

Bayan Kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Najeriya, a karshen makon da ke karatowa ne ake sa ran za a gudanar da zaben gwamnoni.

Yanzu haka hankula sun fara karkata kan yadda batun canja sheka ke zama ruwan dare a Najeriya musamman ma tun baya da jam’iyar adawa ta APC ta lashe zaben shugaban kasa.

“Za mu iya kallon haka ta fuska biyu kodai jam’a da dama sun dawo daga rakiyar jam’iyya mai mulki suna shiga jam’iyar APC domin suna so su ba da gudunmuwarsu.” In ji Tukur Abdulkadir, malami a sashen kuyar da kimiyyar siyasa a jami’ar jihar Kaduna.

Haka kuma ya kara da cewa hakan mai yuwuwa na nufin ba a shirye su ke su zauna a bangaren adawa kamar yadda sauran jam’iyun adawa su ka yi na tsawo shekaru 16 ba.

Ya kuma kore fargabar da ake yi na cewa watakila Najeriya za ta koma mulkin jam’iya guda ya na mai cewa yadda PDP ta karbu ta mallake kusan biyu cikin kashin ukun ‘yan majalisu bai hana samar da jam’iyun adawa ba.

‘Yan siyasa da dama a Najeriya na ta ci gaba da komawa jam’iayr APC yayin da ake shirin tunkarar zaben gwamnoni a ranar 11 ga watannan na Aprilu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG