Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Yobe Ya Mayarwa Dan Takaran PDP Martani


Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe.

Biyo bayan kalamun Maina Waziri dan takarar kujerar gwamna a karkashin PDP gwamnan jihar Yobe ya mayar masa da martani

A fururcin da Alhaji Adamu Maina Waziri, dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin PDP, yace shi da Janar Buhari shugaban Najeriya mai jiran gado, suna da akida daya. Saboda haka zabensa zai kawo masalaha a jihar.

A martanin da gwamnan jihar Ibrahim Geidam ya mayarwa Maina Waziri yace kalamun nashi irin na masu son kawo rudani ne. Yace ko kusa ba za'a iya kwatanta Maina Waziri da Janar Buhari ba. Banda cewa Buhari yayi shugaban kasa kuma an ga kamun ludayinsa ya kuma rike mukamai da dama wadanda yayi anfani dasu domin taimakon jama'a ba tare da almundahana ba. Shi ko Maina menene ya yiwa jama'a.Ko a jihar Yobe me yayi da mutane suka mora? Babu. Yace saboda haka bashi da wani tarihi da zai nuna halinsa daya ne da na Janar Buhari.

Gwamnan ya kara da cewa idan gaskiya ne Maina Waziri yana da akida daya da Janar Buhari to ya bar PDP ya shiga APC. Maganar gaskiya ita ce Maina Waziri bashi da irin halayen Janar Buhari.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG