Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Suka Sa Ake Tunawa Da Janar Murtala


Janar Murtala Muhammed

Cikin kwanaki dari biyu da ya yi yana mulki Janar Murtala Ramat Muhammad ya kafa tubalin sabon kundun tsarin mulki, da tsarin sabuwar gwamnati da ake anfani da shi yanzu, da samar babban birnin tarayya, da yaki da cin hanci da rashawa.

Kimanin shekaru 42 ke nan da Allah ya yi wa Janar Murtala Muhammad rasuwa amma har yanzu ana tunawa da shi sanadiyar abubuwan da ya yi cikin kwanaki 200 da ya yi yana mulki.

A cewar Malam Ibrahim Ado Kurawa, wani masanin tarihi kuma daga jihar Kano - jihar shi marigayin, Janar Murtala mutum ne mai kishin kasa da kaunar jama'arsa da son hadin kan duk 'yan kasar.

Malam Kurawa ya ce Janar Murtala ya lura cewa tsarin mulkin Burtaniya da kasar ta gada a lokacin da aka bata 'yanci shi ne ummul aba'isin rarrabuwar kawunan 'yan Najeriya. A cewarsa, shirin ya tanadi zaben mutum daga garinsu kana ya je tarayya inda yana iya zama shugaban kasa. Wannan shirin ya sa babu shugaban da yake ganin kasar tamkar daya ce sai dai inda ya fito.

Janar Murtala Muhammad shi ya samar da shirin gwamnatin da ake amfani da shi. Haka zalika, shi ya samar da babban birnin tarayya kuma ya dora tubalin samun jam'iyyu da za su nemi tsayawa takara a duk fadin kasar. Shi kuma ya fara aika ma'aikata daga wannan bangaren zuwa wancan ba tare da yin la'akari da inda mutum ya fito ba.

Baya ga wadannan abubuwan, Janar Murtala Muhammad shi ne shugaban Najeriya na farko da ya yi yaki da cin hanci da rashawa gadan-gadan.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG