Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Suka Sa Zan Sake Tsayawa Takara a 2019 - Buhari


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadi dalilan da suka kawadaitar da shi har ya yanke shawarar cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2019.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dalilin da ya sa zai sake tsayawa takara shi ne, saboda "kiraye-kiyaren" da mutane suka rika yi na ya nemi wa'adi na biyu.

Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan sabbin kafafen yada labarai, Alhaji Bahsir Ahmad ne ya bayyana hakan, a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

"Ana shirin tashi (a taron APC) shugaba Buhari ya nemi a bashi abin magana, anan ya tashi ya bayyanawa wadanda suke wurin cewa, bayan kiraye-kiyaren da mutane da suka yi da kuma irin abubuwan da ya kalla suke faruwa a kasar, ya amince, zai sake tsayawa takara." Inji Ahmad.

Buhari wanda ya aka jima ana jiran ya fito fili ya bayyana matsayarsa kan ko zai nemi wa’adi na biyu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ne a wani taron shugabannin jam’iyyarsa ta APC.

A baya-baya nan wasu Gwamnoni sun nuna goyon bayansu ga shugaban, kana wasu kungiyoyi daban-daban su ma sun nuna goyon bayansu kan ya tsaya takara a zaben na badi.

Fadar shugaban kasar ta Aso Rock ta sha kaucewa wannan batu a duk lokacin da aka taso da shi, inda ta kan ce ba batun tsayawa takara ba ne a gaban shugaban.

Rahotannin sun taba bayyana cewa Buhari ya taba nuna wata alama da ke bayyana cewa zai tsaya takara shi ne a lokacin da yake ganawa da al’umar Najeriya mazauna birnin Abidjan a kasar Ivory Coast.

A lokacin ganawar, Buhari, wanda ya makara wajen isa tattaunawar da ‘yan Najeriya, ya ba da hakuri ga mahalarta taron yana mai cewa ya tsaya jiran gwamnonin jihar Akwa Ibom da Bauchi ne, domin mutanensu su gansu, ko hakan zai taimaka mai wajen samun kuri’u a nan gaba.

A kwanakin baya, tsofaffin shugabannin Najeriya, Janar Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Badamasi Babangida, sun fitar da budaddun wasiku suna sukar gwamnatin Buhari.

A cikin wasikun, sun bai wa shugaba Buhari shawara da kada ya nemi takara a 2019, lamarin da ya haifar da cece-ku-cen siyasa.

Obasanjo a tasa wasikar, ya nemi da a samar da wata sabuwar gamayya da za ta iya zama jam’iyyar siyasa a nan gaba, yayin da shi kuma Babangida ya ba da shawarar cewa a ba matasa wuri su jagoranci mulkin kasar.

Da ma masu sharhi a fannin siyasa sun yi hasashen cewa shugaban zai tsaya takara, suna masu cewa jinkirin bayyana hakan da ya yi, jira yake ya samu lokacin da ya fi dacewa.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin jin cikakkiyar hirarsa da Alhaji Bashri Ahmad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG