Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalililn Gayyatar 'Yan APC a Majalisar Dokokin Kasa Aso Rock


Shugabancin Jamiyyar APC mai mulki ya kira taron majalisar dokokin kasa a Fadar Aso Rock kan za6en fidda gwani kai tsaye.

Sanata mai wakiltan Mazabar Shugaban Kasa Mohammadu Buhari a majalisar dattawa Ahmed Babba Kaita ya ce an gayyace su ne zuwa fadar shugaban kasa akan kalamai masu karo da juna da suke samu musamman daga 'ya'yanta a majalisar kan batun tilasta wa jam'iyyyun siyasa zaben 'yan takararsu ta hanyar za6en fidda gwani kai tsaye.

Babba ya ce taron yana da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa, majalisa da jamiyya, amma ya yi tir da irin take taken da gwamnoni ke yi da ke nuni da cewa su ne suke ragamar Jamiyyar, wato sai abinda suke so ko kuma suka gadama shi za a yi a jamiyance.

Babba ya kara jaddada cewa 'yan majalisa suna kokari ne na kare muradun 'yan Najeriya wadanda har yanzu gwamnoni ba su ba su daman more romon dimokradiya ba, inda yayi misali da yadda suke so su ja akalar jamiyyar, kuma suke so su rika zaban duk wanda suke so ba tare da bin ka'ida ba.

Babba ya ce ana da tsofaffin gwamnoni a majalisar datawa, kuma za a cigaba da samun gwamnonin, domin duk wanda yake majalisa yana iya zama gwamna.

Babba ya kara tunatar da dukan wadanda suka halarci taron da cewa su tuna irin matakin da yan Najeriya suka dauka akan jamiyyar PDP da ta yi shekaru 16 tana mulki a kasar, domin sai da yan kasa suka kai ta kasa, inda yake ganin wai irin kama karyar da ake yi a APC yanzu ya ma fi wanda aka yi a PDP, kuma in ba a yi hankali ba, za a yi wa APC irin abinda aka yi wa PDP ko fiye da haka, domin za a iya yin kaca kaca da APC.

Babba ya ce Shugabanin APC ba su ji dadin abin da aka fada masu a wurin taron ba, amma yana ganin in kunne ya ji to gangan jiki ya tsira.

Saurari cikakken hirar a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:04 0:00

XS
SM
MD
LG