Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Bola Tinubu Ya Kai Ziyara Kano


Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagora a jam’iyyar APC mai mulki Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya isa birnin Kano domin wata ziyara ta musamman.

Yayin wannan ziyara, ana sa ran Tinubu zai gana da majalisar sarakunan gargajiya ta arewa a ranar Litinin.

Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da yake shirin yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya tsara zai yi a birnin na Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce Tinubu har ya kai wa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ziyarar ban-girma a ranar Lahadi gabanin tattaunawar da zai yi da majalisar sarakunan gargajiyar.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya mai jagora zuwa fadar sarkin.

Buhari, (dama) da Tinubu, (hagu)
Buhari, (dama) da Tinubu, (hagu)

Masu lura da al’amuran siyasa sun ce ga dukkan alamu, Tinubu ya fara sharar fage ne dangane da burinsa na neman mukamin shugaban kasa a zaben 2023, ko da yake, bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba.

Karin bayani akan: Sarkin Kano, Tinubu, Alhaji Aminu Ado Bayero, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin wata hudu da tsohon gwamnan na Legas wanda zai cika shekara 69 ya kai ziyara jihar ta Kano.

Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Tinubu ya fadawa Sarkin Kano cewa ziyarar tasa “wani yunkuri ne na kara hada kan kasa da kuma ganewa idonsa irin ci gaban da aka samu a jihar ta Kano.”

Rahotanni sun ce kungiyar tuntuba ta matasa ta Arewa Youth Consultative Forum ta nuna adawarta da wannan ziyara ta Tinubu.

A farkon makon da ya kare an yi ta yamadidin cewa an samu baraka a tsakaninsa da shugaban kasa Shugaba Muhammadu Buhari, batun da fadar gwamnati ta Aso Rock ta musanta.

XS
SM
MD
LG