Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Saki El Zakzaky Da Matarsa


Sheik El-Zakzaky
Sheik El-Zakzaky

Tun a shekarar 2015 ake tsare da El Zakzaky da matarsa bayan wani sabanı da aka samu tsakanin mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Islamic Movement of Nigeria IMN da dakarun Najeriya.

Wata babbar kotu a jihar Kaduna, ta wanke Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa Zeenat wadanda tuni aka sake su.

Yayin da yake karanto mataysar kotun a zaman da ta yi a ranar Laraba, Alkali Gideon Kurada ya ce masu shigar da kara sun gaza gabatar da kwararan hujjojin da suka nuna El Zakzaky da matarsa sun aikata laifukan da ake tuhumar su akai.

Gwamnatin jihar ta Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta zargi El Zakzaky da matarsa da laifin aikata kisa da yin gangamin da ya saba doka da kuma ta da zaune tsaye.

Tun a shekarar 2015 ake tsare da El Zakzaky da matarsa bayan wani sabanı da aka samu tsakanin mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Islamic Movement of Nigeria IMN da dakarun Najeriya.

Lamarin ya faru ne a Zaria a zamanin tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya.

Mabiya kungiyar ta IMN sun yi zargin na kashe masu almajirai da dama a lokalin, zargin da sojojin Najeriyar suka sha musantawa.

Mabiya kungiyar ta IMN sun yi ta gudanar da zanga-zanga a Abuja a lokuta daban-daban cikin tsawon lokacin da malamin ya kasnace a tsare, inda a nan ma an sha yin artabu tsakanin mabiyan kungiyar da jami’n tsaron Najeriya.

Gabanin wannan matsaya da kotun ta dauka, babban lauyan da ke kare El Zakzaky Mr Femi falana, ya yi korafin cewa dukkan shaidun da masu shigar da kara suka gabatar don tuhumar malamin, sun gaza danganta El Zakzaky da matarsa da laifukan da ake tuhumar su akai.

An dai gudanar da shari’ar ne karkashin tsauraran matakan tsaro.

XS
SM
MD
LG