Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Mbaka Ya Ce Buhari Ya Sauka Ko A Tsige Shi


Rev. Father Ejike Mbaka (Instagram/ejikembaka)

“Ta ya ya mutane za su yi ta mutuwa, sannan babban mai tsaron kasa zai zauna ba tare da ya ce uffan ba.” Mbaka ya fadawa taron mabiyansa.

Limamin Katolika, Rev. Father Ejike Mbaka, ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki.

Mbaka ya yi wannan kira ne daga cocin da yake jagoranta ta Adoration Ministry da ke jihar Enugu a kudu maso gabashin Najeriya, inda ya ce idan Buhari ya ki sauka, ya kamata a tsige shi.

“Ta ya ya mutane za su yi ta mutuwa, sannan babban mai tsaron kasa zai zauna ba tare da ya ce uffan ba.” Mbaka ya fadawa taron mabiyansa a ranar Laraba.

Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)
Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)

Shi dai limamin ya kasance daya daga cikin fitattun mutane da suka nuna goyon baya ga shugaba Buhari a lokacin zaben 2015.

“Bari na fada muku, idan da a wata kasa ce da ta ci gaba, da Buhari ya yi murabus idan aka yi la’akkari da abin da ke faruwa. Abin mamaki ne a ce ya zauna kyam yayin da ake kashe mutane.”

Karin bayani akan: jihar Enugu, DSS, ISWAP, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Jama’a da dama za su yi mamakin kalaman Limamin lura da cewa masoyin Buhari ne, asali ma sun sha ganawa tare da shugaban.

Hukumar DSS ta taba tsare Salihu Tanko Yakasai, hadimi a gwamnatin gwamna Ganduje na Kano, saboda ya soki gwamnatin Buhari (Hoto: Shafin Twitter Salihu Tanko-Yakasai)
Hukumar DSS ta taba tsare Salihu Tanko Yakasai, hadimi a gwamnatin gwamna Ganduje na Kano, saboda ya soki gwamnatin Buhari (Hoto: Shafin Twitter Salihu Tanko-Yakasai)

Sai dai a lokuta da dama, suka irin wannan a baina jama’a kan janyowa masu yenta fushin hukumomi, domin a ko a ranar Laraba hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tsare fitaccen dan siyasa Dr. Usman Bugajehar tsawon sa’a takwas, saboda ya soki gwamnatin Buhari kan yadda matsalar tsaro ta dabaibaye kasar.

Kalaman Father Mbaka na zuwa ne, a daidai lokacin da dan majalisar wakilai Dachung Bagos da ke wakiltar mazabar Jos South/Jos East ya ce, majalisar dokoki za ta duba yiwuwar tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan har al’amura ba su sauya ba.

Bagos ya fadi hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis.

Najeriya ta shiga matsanancin matsalar tsaro musamman a arewa maso yammci da gabashi, inda ‘yan bindiga ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa, yayin da a gefe guda kuma kungiyar Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kai hare-hare gabashin arewacin kasar.

'Yan Bindiga Suka Yi Hedikwatar 'Yan Sanda A Owerri
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

Harin da 'yan bindiga suka kai yahedikwatar 'yan sanda a Owerri.

A kudancin kasar ma rahotanni na nuni da cewa al’amura na kara dagulewa, inda ‘yan bindiga suke cin karensu ba babbaka, ta hanyar kai hare-hare akan jami’an tsaro da hukumomi, baya ga kisan gilla da ake zargin ‘yan kungiyar ‘yan aware ta IPOB ke yi wa makiyaya a yankin.

Ko a karshen makon da ya gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan gidan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

A makon da ya gabata ne Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga da ke kai hare-hare akan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci irin wannan ta’asa ba.

'Yan Najeriya Masu Gudun hijira a Nijar
'Yan Najeriya Masu Gudun hijira a Nijar

“Ya zama dole a dakata da irin wannan mummunan danyen aiki na rashin hankali da ake yi akan mutanen da ba su san hawa ba balle sauka.” Wata sanarawa da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya fitar a lokacin harin da ya kashe gomman mutane a Zamfara ta ce.

“Ya kamata masu aikata wadannan manyan laifuka, su daina gani kamar gwamnmati ba ta da karfin da za ta murkushe su.”

Garba Shehu ya ce shugaban na Najeriya, ya ba jami’an tsaro umurnin su dauki matakan gaggawa wajen magance hare-haren ‘yan bindigar.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG