Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Muka Sauya Taken Yaki Da Boko Haram – Buratai


Buratai

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya ce dalilin da ya sa aka sauya taken yaki da kungiyar Boko Haram daga “Operation Zaman Lafiya” zuwa Operation “Zaman Lafiya Dole” shi ne domin su sauya tunanin dakarunsu a yakin da su ke yi.

An dai nada Buratai ne a shekarar da ta gabata bayan da jam’iyar APC da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta samu nasara a zaben da aka yi a bara.

Shugaba Buhari ya gaji yaki da kungiyar ta Boko Haram ne daga tsohon shugaba Goodluck Jonathan, wanda shima ya gada daga marigayi tsohon shugaba Umaru Musa ‘Yar adua.

Rikicin na Boko Haram ya samo asali ne tun daga shekarar 2009, ya kuma yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 20, sannan ya raba kusan mutane miliyan biyu da gidajensu.

Saurari cikakkiyar hirar da Ibrahim Alfah Ahmed ya yi da Buratai yayin ziyarar da ya kawo ofishinmu da ke birnin Washington.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG