WASHINGTON D.C. —
Rudunanar sojin Najeriya ta "Operation Lafiya Dole" ta mika wasu yara da ake zaton cewa suna da alaka da 'yan kungiyar Boko Haram su 25 ga gwamnatin jihar Borno.
Rundunar ta ce ta kama su ne tare da iyayensu a ci gaba da yaki da take yi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Kwamandan rudunar sojin ta operation lafiya Dolen, Manjo Janar Olusegun Adeneyi ne ya mika yaran da suka hada da 'yan mata biyu da maza 23 ga gwamnatin jihar Borno.
A kwanakin baya, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi korafi kan yadda ake samun wasu kungiyoyin tsaro na sa-kai da na 'yan ta'adda suke tilastawa kananan yara shiga aikin soji.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 01, 2023
Tinubu Ya Gana Da Shugabanin Tsaro a Karo Na Farko